Commons:Wiki Loves Monuments/Binciken DEI 2022/Rahoton ƙarshe
Bayani | Gabatarwa | Abin koyo | Shawarwari | Matsalolin da za'a iya fuskanta | Me ke cikin batutuwan? | Ƙarin bayanai |
- Game da Wiki Loves Monuments
Wiki Loves Monuments (WLM) wata gasa ce ta kowa da kowa akan ababen tarihi na al'adu, da Rassoshin Wikimedia da ƙungiyoyi suke shiryawa. A 2010 an shirya shi ne a Netherlands, sai ya biyo baya da shirye-shiryen da damar su a ƙasashen Turai karo na 2011. Tun wannan lokacin 2012 gasar ana shirya sa a duk shekara a ƙasashen duniya da dama! Wannan ne mafi girman gasar ɗaukar hoto da ake yi a duniya kuma ana saran a ƙirga shi cikin masu samun mahalarta da yawa a wannan shekara.
Burin gasar itace ana buƙatar mutane baki ɗaya —makaranta da masu sakai a Wikipedia, masu ɗaukar hoto, masu son annashuwa, da sauran su.— da su ɗauki hotunan wuraren tarihi da ɗaura su a wikimedia Commons don amfani dasu a Wikipedia da wasu manhajoji na Wikimedia.
- Game da wannan rehoton
Tawagar Wiki Loves Monuments na duniya sun sanya ayi wannan binciken daga kuɗin 2021-2022 grant daga Wikimedia Foundation. mai-binciken yayi aiki daga Oktoba 2021 - Augusta 2022 kuma yayi tattaunawa da mawakilta daga tawagar kasashe 20, waɗanda sun jima da sabbin halarta gasar na ɗaukar hoto a duk shekara.
Ƙarin bayani game da wannan binciken na farko da tattaunawar da aka yi za'a iya samun su a mid-term report daga Afrilu 2022.